Jam’iyyar APC A Najeriya Ta Tabbatar Da Tinubu A Matsayin Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam’iyyar A Shekara Ta 2027

Jam’iyyar ‘All Progressives Congress” (APC) mai Mulki a tarayyar Najeriya ta tabbatar da shugaban Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban

Jam’iyyar ‘All Progressives Congress” (APC) mai Mulki a tarayyar Najeriya ta tabbatar da shugaban Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar Jam’iyyar a zaben shugaban kas ana shekara ta 2027 mai zuwa.

Shafin yada labarai na Afrika ya bayyana cewa a jiya Alhamis ce a taron Jam’iyyar wanda aka gudanar a Abuja, kuma wanda ya zo dai-dai da cika shekaru biyu da zagayensa na farko na shugabancin kasar Jam’iyyar ta nada shi Shugaba Bola Ahmed Tinubu dan shekara 73 a duniya a matsayin dan takararta a zaben na shekara ta 2027, don ya sami damar kamala shirinsa nag yare-gywaren tattalin arzikin kasar da y afara.

Shugaban Tinubu dai ya kara farashin man fetur a ranar da ya hau kan kujerar shugabancin kasar, ya kuma cire tallafin da gwamnati take yiwa farashin man, sannan ya kara haraji wanda duk sun hadu sun Sanya rayuwar mafi yawan mutanen kasar cikin bala’I wanda basu taba ganin irinsa .

Shirin nasa ya dadadawa manya-manyan cibiyoyin kudade a duniya wadanda ba ruwansu da rayuwar talaka a ko ina suke a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments