Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Karfin Tsaro Da Makamansu Masu Linzami Ne Suka Hana Makiya Kai Musu Hari

Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi

Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin tsaron Iran da makamanta masu linzami suna ba su ƙarfin gwiwa

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa, da a ce Amurka za ta iya lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba za ta shiga zaman tattaunawa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ta dogara da karfin sojanta, kuma shi ne ya tilasta wa makiya zaman tattaunawa da ita.

A ziyarar da ya kai wajen baje kolin littafai na birnin Tehran, Araqchi ya ce dangane da tattaunawa wand aba na kai tsaye ba da Amurka: Idan da a ce Amurka na da karfin lalata cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, da ba ta shiga tattaunawa ita ba.

Araqcgi ya kara da cewa: Iran ta dogara da karfinta na soji ne lamarin da ya tilastawa makiya zama kan teburin tattaunawa da ita, yana mai cewa karfin kariya da makamai masu linzami na Iran yasu bai wa masu shiga tsakani na Iran damar yin shawarwari domin suna hana bangaren da ke makiya gudanar da duk wata kasada ta soja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments