Kakakin majalisar dokokin jihar Edo, Blessing Agbebaku, ya bayyana dalilansa na sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
In ba a manta ba, kakakin majalisar Agbebaku, tare da wasu ‘yan majalisar biyu, Hon. Sunday Fada Eigbiremonlen da Hon. Idaiye Yekini Oisayemoje, a ranar Talata sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
- Nijar Ta Soke Yarjejeniyar Tattara Bayanai Da Rasha Da Turkiyya, Ta Fara Neman Sabbin Abokan Hulɗa
- Za Mu Magance Matsalar Ruwan Sha Kafin Ƙarshen 2025 A Kaduna – Uba Sani
A yayin da yake sanar da ‘yan majalisar cewa ya sauya sheka a hukumance a ranar Laraba, Agbebaku ya ce ya koma jam’iyyar APC ne domin ya ci gaba da samun ribar ofishin kakakin majalisar domin ci gaban mazabar sa.
Ya ce, “Na koma jam’iyyar APC ne domin in ci gaba da samun ribar kujerar kakakin majalisar domin ci gaban mazaba ta.
“A gare ni, sauya sheka ba batun jam’iyya ba ne, illa don ci gaban mazaba ta, a matsayina na mai wakiltar mutane na, idan na jefar da wannan matsayi saboda jam’iyya, matsayin da zai bunkasa ci gaban yankina, hakan na nufin ban shirya yi wa jama’a aiki ba.
“’Yan uwana na majalisa, ina so in sanar da wannan majalisa a hukumance cewa, kakakin majalisar, Rt. Hon. Blessing Agbebaku, ya koma APC,” inji shi.
Agbebaku ya bayyana cewa ‘yan mazabar sa na goyon bayan matakin da ya dauka, inda ya ce “akwai ayyukan ci gaba a mazabar Owan ta Yamma wanda Gwamna Monday Okpebolo ya kaddamar.”
Ya kara da cewa, “Don haka, sauya sheka na ba wai don wata manufa ta kashin kai ba ce, sai dai sadaukar da kai ga wadanda suka zabe ni, muradin al’ummata ne gaba a don da izininsu nake zaune anan yau,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp