Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne sun kai hari kan wani jirgin ruwa da ke jigilar mata ’yan kasuwa zuwa Ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudancin Jihar Bayelsa, a kan hanyar ruwan Lobia/Foropa.
Rahotanni sun ce maharan sun yi garkuwa da wasu mata huɗu a lokacin da lamarin ya faru a ranar Talata.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta
- Najeriya za ta karɓi baƙuncin Gasar Karatun Alkur’ani ta Duniya a karon farko
Wata majiyar unguwar da lamarin ya faru ta shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Alhamis, maharan sun kai harin ne ’yan mintuna kaɗan bayan jirgin ruwan fasinjan ya tashi daga gaɓar ruwan Swali a Yenagoa, babban birnin jihar.
Ya ce, kimanin mutane 12 da ke cikin kwale-kwalen an ƙwace dukiyoyinsu da kuɗaɗensu, yayin da ’yan fashin suka yi awon gaba da huɗu daga cikin matan zuwa cikin daji ba tare da sanin dalilansu ba.
A halin yanzu, Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Ijaw ta kudu ta 4 a majalisar dokokin Jihar Bayelsa kuma shugaban kwamitin kare haƙƙin ɗan Adam na majalisar Honorabul Selekaye Victor-Ben, ya yi Allah wadai da lamarin.
Ya kuma bayyana sace mutanen a matsayin harin da aka kai wa waɗanda ba su ji ba ba su gani ba.
A cewarsa, “Ba wai cin mutuncin bil’adama ba ne kawai, har ma da babbar barazana ga zaman lafiya da tattalin arzikin mazaɓarmu da ma jihar baki ɗaya.
“Ina yin Allah wadai da wannan ta’addanci da kakkausar murya kuma ina bayar da haɗin kai tare da iyalan waɗanda abin ya shafa a wannan lokaci mai tsanani.”
Ya kuma yi kira ga gwamnatin Jihar Bayelsa da dukkanin hukumomin tsaro da abin ya shafa, musamman rundunar ’yan sandan Najeriya da su gaggauta sakin waɗannan matan da aka sace ba tare da wani sharaɗi ba.