Gwamnatin jihar Yobe ta karyata wani rahoto da ake yadawa a kafafen sada zumunta, inda ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram na tururuwar zuwa Damaturu, babban birnin jihar.
Mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin tsaro, Brig.-Gen. Dahiru Abdulsalam (mai ritaya), a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana rahoton a matsayin karya, yaudara, yana mai alakanta shi da shirin marasa kishin kasa da ke neman tada zaune tsaye a jihar.
- Hanyoyin Warware Matsalolin Ma’aurata(1)
- Kofin Duniya 2026: Kasashen Da Suka Samu Tikitin Shiga Gasar Zuwa Yanzu
A cewar Abdulsalam, bayanan da aka yada dake cewa, Boko Haram na tafiya zuwa Damaturu ba daga ofishinsa ya fito ba, na karya ne kuma ya kamata a yi watsi da shi gaba daya kuma ba shi da tushe.
Ya kuma bukaci jama’a musamman mazauna Damaturu da su kwantar da hankulan su, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.
Abdulsalamu ya bada tabbacin aniyar gwamnati na wanzar da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya yi gargadi kan yada labaran karya da ka iya haifar da firgici a tsakanin ‘yan kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp