Leadership News Hausa:
2025-09-17@23:15:07 GMT

Tarihi: Mugunta Ba Za Ta Iya Lashe Adalci Ba

Published: 9th, September 2025 GMT

Tarihi: Mugunta Ba Za Ta Iya Lashe Adalci Ba

Kana wasu alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, a cikin watanni 7 na farkon wannan shekara, darajar kayayyakin da kasar Sin ta shigo da su daga kasashe mafi karancin ci gaba a nahiyar Afirka, wadanda Sin ta riga ta yafe musu dukkan haraji, ta kai dalar Amurka biliyan 39.

66, adadin da ya karu da kaso 10.2 cikin dari bisa na makamancin lokacin a bara. Ta hanyar karfafa hadin gwiwar cinikayya da abokan hulda kamar Sin, da inganta cinikayya a cikin nahiya, ana sa ran ganin Afirka za ta samu nasarar rage tasirin manufar harajin Amurka.

A halin yanzu, kasashe masu tasowa, ciki har da kasar Sin da kasashen Afirka, suna kokarin daukaka ra’ayin cudanyar sassa daban daban, da na bude kofa, da yin hadin gwiwa tare da tabbatar da moriyar juna, da hadin kai da juna, a karkashin laimar tsare-tsaren hadin gwiwa irin na BRICS, kuma suna tafiya zuwa gaba kan wata turba mai adalci. Tabbas babu wani karfi da zai iya hana su cimma buri da samun nasara. (Bello Wang)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta

Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana, tare da amsa tambayoyin manema labarai.

A cewar bayanan da aka gabatar a yayin taron, ayyukan tattalin arzikin kasar a watan Agusta sun samu ci gaba ba tare da tangarda ba. Kuma hakan ya bayyana ne ta hanyoyi daban-daban kamar haka: masana’antu sun habaka cikin sauri, masana’antar kera kayayyakin aiki da masana’antar fasaha sun samu ci gaba mai kyau. Kana ayyukan bayar da hidima su ma sun bunkasa cikin sauri. Baya ga haka, an samu ci gaba mai kyau a bangaren bayar da hidimomi na zamani. Harkokin kasuwanci sun samu ci gaba cikin natsuwa, inda harkokin sayar da kayayyaki ga masu sayayya suka kara habaka. Har ila yau, kadarorin jari sun ci gaba da karuwa, jarin masana’antu ya habaka cikin sauri, harkokin fice da shigen kayayyaki sun ci gaba da girma, tsarin kasuwanci ya ci gaba da ingantuwa, kana yanayin samar da guraben aikin yi, ya kasance kan wani mataki mai daidaito. Sai dai kuma saboda yanayin da ake ciki, adadin marasa aikin yi a birane ya karu, ma’aunin Core CPI ya ci gaba da hauhawa, kana faduwar farashin kayayyakin masana’antu ya ragu.

Bayanan sun kara da cewa, akwai bukatar lura da cewa, ana fuskantar yanayin rashin tabbas a waje, kuma tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar kalubale da hadari da yawa. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
  • An Bude Dandalin Tattauna Batutuwan Tsaro Na Xiangshan Karo Na 12 A Beijing 
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Hadin Gwiwar Raya Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Makamashi Tsakanin Sin Da Rasha Ba Abun Zargi Ba Ne
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta