MDD ta buƙaci hukumomin Najeriya su kamo waɗanda suka kai hari a Bama
Published: 8th, September 2025 GMT
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da harin da ’yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, da ke yankin Bama na Jihar Borno.
Harin wanda ya faru a yammacin ranar Juma’a 5 ga watan Satumba ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 60 tare da sace wasu da dama ciki har da sojoji da fararen hula.
A wata sanarwa da Mohamed Malick Fall, babban jami’i mai kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya fitar, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin.
MDD ta yi kira ga hukumomin Najeriya da su gano waɗanda suka kai wannan harin tare da ɗaukar mataki a kansu.
Fall ya ce: “Ina kira ga hukumomin tsaro da su kamo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aikin. Ina kuma kira da a gaggauta ceto duk waɗanda aka sace.”
Yarima Harry ya ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth II Matatar Dangote ta musanta dakatar da aiki“Ina matuƙar baƙin ciki da rahoton kisan da aka yi wa sojoji da fararen hula da dama a ranar Juma’a a ƙauyen Darajamal da ke ƙaramar hukumar Bama a Jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya”
A madadin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, Fall ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda harin ya shafa, gwamnati, da kuma al’ummar Jihar Borno, tare da yi wa waɗanda suka ji rauni fatan samun sauƙi cikin gaggawa.
Rahotannin sun ce an kashe fararen hula fiye da 60, inda ake zargin an yi garkuwa da waɗanda ba a san adadinsu ba.
Wasu da dama sun tsere, kuma gidaje fiye da 20 sun ƙone ƙurmus a harin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Harin Bama Harin boko haram waɗanda suka
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Matakin hana malaman da ba su da rajista hawa mumbari a Neja yana ci gaba da yamutsa hazo a ciki da wajen jihar.
Yayin da wasu suke ganin wannan mataki bai dace ba, wasu kuwa gani suke faduwa ta zo daidai da zama, wato matakin ya zo a daidai lokacin da ake bukata.
NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau UkuShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kan tanadin Dokar Kasa game da wannan batu.
Domin sauke shirin, latsa nan