Araqchi: Ya Soki Kasashen Turai Game Da Gum Da Baki Kan Shirin Nukiliyar Isra’ila
Published: 8th, September 2025 GMT
Sayyid Abbas Araqci ministan harkokin wajen kasar iran a wani sakon mayar da martani da ya aike da shi game da shirun da kasashen turai suka yi kan fadada shirin nukiliyar HKI ya jaddada cewa yin shiru da baki da suka yi ya nuna cewa yanzu basu da wata dama ko kwarin guiwar yin Magana kan hana yaduwar makamin nukiliya kan kowacce kasa .
Rahotan ya bayyana cewa Araqchi ya bayyana a shafinsa na x cewa batun samuwa ko fadada shirin makamin nukiliya ba shi ne a gabansu ba, lamarin shi ne waye ya bada dama a samu ci gaban ilimi ko da ma na shirin nukiliya na zaman lafiya ne,
Ya jaddada cewa saboda haka wannan ba’a bin mamaki ba ne gum da baki da kasashen turai suka yi game da fadada shirin kera makamin nukiliya da HKI ta yi a yankin mu, wato makamin nukiliya yana hannu abokan burmisu da suke kisan kare dangi,
Daga karshe ya nuan cewa kila kasashen turai guda Uku da Amurka su karyata amma shirunsu yasa basu da wani sauran karfin guiwa na yin Magana kan lamarin .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jagora: Wajibi Ne Kasashen Musulmi Su Yanke Alakarsu Da Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya September 8, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Muhimmancin Shawarwarin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci September 8, 2025 Admiral Sayyari: Dole Ne Jami’an Tsaron Iran Su Kasance Cikin Shirin Ko-Ta Kwana September 8, 2025 Hamas Tana Maraba Da Duk Wata Shawarar Da Zata Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci Kan Gaza September 8, 2025 Dakarun Yemen Sun Kai Farmaki Kan Muhimman Yankuna Daban-Daban Na ‘Yan Sahayoniyya September 8, 2025 Isra’ila tace Ta Yi Kokarin Kashe Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci A Yakin Kwanaki 12 Da Iran September 7, 2025 Iran Ta Kirayi E3 Su Koma Kan Hanyar diblomasiyya September 7, 2025 Iran: Zahra Kiyani Ta Lashe Lambar Zinari A Gasar Wushu A Karon Farko September 7, 2025 Jiragen Yaki Marasa Matuka Na Yemen Sun Fada Kan Filin Jiragen Sama Na Ramon A Isra’ila September 7, 2025 Wilayati: Yanci da Tsaron Kasar Iraki Na Da Matukar Muhimmanci Ga Iran September 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamin nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan
Isra’ila ta amince da gina sabbin gidaje 1,300 a yankin Gush Etzion, kudu da Gabashin Urushalima da ta Mallake, wanda hakan ke nuna wani sabon ci gaba da fadada matsugunai ba bisa ka’ida ba a fadin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye.
A cewar tashar talabijin ta Isra’ila Channel 14, Kwamitin tsare-tsare da Gine-gine na musamman da ke kula da matsugunan da ke Gush Etzion ya amince da wannan shawara a farkon wannan makon, inda ya shafi unguwar Har HaRusim, wadda ke kusa da matsugunan Alon Shvut, kudu maso yammacin Gabashin Urushalima da aka Mallake.
Shirin bai shafi gidaje ba kawai, har ma da gina makarantu, wuraren jama’a, wuraren shakatawa, da kuma babbar cibiyar kasuwanci da aka yi niyya don yi wa al’ummomin da ke makwabtaka hidima.
Majalisar Yankin Gush Etzion ta yi maraba da wannan mataki, tana mai ganin hakan a matsayin martani ga karuwar bukatar mazauna yankin.
Wannan sanarwar ta zo ne kwanaki kadan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi watsi da damuwar da ake da ita game da ayyukan Isra’ila a Yammacin Kogin Jordan.
Jawabin Trump ya zo ne a daidai lokacin da majalisar dokokin Isra’ila ta Knesset ta amince da wasu kudirori biyu da nufin hade Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye da kuma yankin Ma’ale Adumim.
Irin wadannan matakai za su ware Gabashin Kudus daga yankunan Falasdinawa da kuma raba Yammacin Kogin Jordan zuwa yankuna biyu daban-daban, don haka za su kawo cikas ga yiwuwar hadewar kasar Falasdinu.
Majalisar Dinkin Duniya da yarjejeniya kasa da kasa sun sha nanata cewa matsugunan Isra’ila a yankin Falasdinawa da aka mamaye haramtattu ne a karkashin dokokin kasa da kasa, gami da Yarjejeniyar Geneva ta Hudu.
Bugu da kari, kungiyar kare hakkin dan adam ta Peace Now ta bayyana shirin E1 a matsayin “mummunan rauni” ga samar da Falasdinu, tana mai jaddada cewa aiwatar da shi zai kawo cikas ga yunkurin kafa kasar Falasdinawa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Kasar Czech Ta Hana Wa Wani Sojan HKI Shiga Kasar Bisa Gargadin Faransa October 30, 2025 Sojojin HKI Sun Kutsa Kudancin Lebanon October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci