Ambaliyar Ruwa: NEMA ta ceto mata 2 da jaririya a Kaduna
Published: 7th, September 2025 GMT
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta ce ta samu nasarar ceto wasu mata biyu da wata jaririya da ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Kaduna.
Shugabar hukumar, Hajiya Zubaida Umar ce, ta bayyana hakan a shafinta na Facebook.
Harin Boko Haram: Zulum ya kai ziyarar jaje garin Darajamal Tsadar Rayuwa: NLC ta buƙaci gwamnati ta sake duba albashin ma’aikataTa ce ambaliyar ta auku ne sakamakon ruwan sama mai yawa da aka yi a ranar Juma’a.
Ta ce sama da gidaje 160 da magidanta 500 ne ambaliyar ta shafa a unguwanni irin su Kabala Doki, Bachama, Kigo, Ramat, da Unguwar Dosa/Nasarawa/Mali.
Rahoton ya nuna cewa ruwan kogin Kaduna ne ya yi sama, ya shiga unguwanni, lamarin da ya haddasa ambaliyar.
Shugaban NEMA na Kaduna, Malam Suleiman Mohammed, ne ya jagoranci aikin ceto tare da haɗin gwiwar hukumomin agaji na jihar.
NEMA, ta ce za ta ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin agaji domin tallafa wa waɗanda ambaliyar ta shafa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Jaririy
এছাড়াও পড়ুন:
Sabbin ‘Yan Saman Jannatin Kasar Sin Sun Shiga Tashar Sararin Samaniya Ta Kasar
Ofishin kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane na kasar Sin ya ce, an harba kumbon Shenzhou-21 mai dauke da ‘yan sama jannatin kasar Sin 3 cikin nasara, a daren jiya Juma’a, agogon Beijing.
Daga baya kumbon ya sarrafa kansa wajen hade jikinsa da na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ta yadda ‘yan saman jannatin suka shiga tashar, inda tsoffin ‘yan saman jannati 3 da suka dade a cikin tashar, suka yi musu maraba. Hakan ya shaida haduwar sabbi da tsoffin ‘yan sama jannatin kasar Sin karo na 7 a tashar binciken sararin samaniya ta kasar.
Bisa shirin da aka yi, wadannan ‘yan sama jannati 6 za su kwashe kimanin kwanaki 5 suna aiki tare a cikin tashar, kafin tsoffin ‘yan saman jannatin 3 su kama hanyar dawowa gida.
Zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ‘yan sama jannati 44 zuwa sararin samaniya. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA