Araqchi: Suna Ci Gaba Da Musayar Sakonni Da Amurka Ta Hanyar Masu Shiga Tsakani
Published: 7th, September 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Iran tana ci gaba da musayar saƙon da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani
Ministan harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Araqchi ya sanar da cewa: Ana ci gaba da musayar sakwanni da Amurka ta hanyar masu shiga tsakani, yana mai jaddada cewa, Iran za ta kasance a shirye don yin shawarwari a lokacin da Amurka ta nuna aniyar ta na shiga tattaunawa bisa mutunta juna, matukar dai an mutunta hakki da muradun al’ummar Iran.
A yayin da yake jawabi a zaman taron kasa kan samun damar zuba jari a yankunan ‘yanci da cinikayya a kasar Iran a ranar Asabar, Araqchi ya ce: Yankin Shenzhen na kasar China ya kasance wani karamin kauye ne kawai na kamun kifi, amma a yau ya rikide ya zama daya daga cikin muhimman cibiyoyin fasaha da cinikayya a duniya bayan da kasar China ta fuskanci matsin lamba daga kasashen duniya. Ya kara da cewa Iran na fuskantar irin wannan yanayi, kuma tarihi ya tabbatar da cewa al’ummomin da suka zabi kirkira maimakon mika wuya sun share fagen samun ci gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamandan Sojojin Iran Ya Jaddada Wajabcin Kasancewar Iran Cikin Shirin Yaki September 7, 2025 Shugaban Hukumar Shari’ar Iran Ya Ce: Iran Ba Za Ta Taba Mika Kai Bori Ya Hau Ba September 7, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwata Da Kisan Kiyashi Kan Falasdinawa A Zirin Gaza September 7, 2025 Shugaban Tunusiya Ya Jaddada Bukatar Raya Nahiyar Afirka Ta Hanyar Bunkasa Tattalin Arzikinta September 7, 2025 An Kaddamar da kungiyar tallafawa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka September 6, 2025 Araghchi ya Tattauna da takwarorinsa na kasashen Girka da Slovenia da Saliyo September 6, 2025 Gaza : Adadin Wadanda sukayi shahada a hare-haren Isra’ila cikin sa’o’I 24 ya karu September 6, 2025 Kungiyoyin gwagwarmaya sun fusata da barazanar Isra’ila na bude “kofofin jahannama” a Gaza September 6, 2025 Iran ta aike da kayayyakin jin kai tan 100 zuwa Afghanistan September 6, 2025 Ammar Hakeem ya gana da larijani a nan birnin Tehran . September 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Burkina Faso: Masu Ikirarin Jihadi Sun Kashe Fararen Hula 50 A Cikin Watanni Hudu
Hukumar kare hakkin bil’adama ta “Human Right Watch” ta fitar da wani rahoto da a cikin ta bayyana cewa; kungiyar nan mai ikirarin jihadi a kasar Burkina Faso, ( Jama’at Nusratul-Islam wal Muslimin) da kuma kungiyar Daular Musulunci a cikin yankin Sahara, sun kashe fararen hula 50 daga watan Mayu zuwa yanzu.
Rahoton ya ci gaba da yin bayanin cewa, a cikin Ogusta kungiyoyin na masu riya cewa suna yin jihadi sun kashe mutane 40 a cikin garuruwan Djibo da Youba.
Rahoton ya kuma ce; a watan Yuli kuwa kungiyar IS ta kai wa fararen hula hari da suke kan hanyar kai kayan agaji zuwa garin Gorom-Gorom da aka killace da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 9.
Kungiyar kare hakkin bil’adama din ta ce, wadannan irin hare-haren sun sabawa dokokin kasa da kasa na jin kai, kuma suna a matsayin laifukan yaki.
Kungiyar kare hakkin bil’adaman ta “Human Right Watch” ta mika sakamakon binciken da ta gabatar ga hukumomin tsaro da na shari’a na kasar ta Burkina Faso. Sai dai har yanzu babu wani martani da ta samu.
Shekaru 3 kenan da kasar ta Burkan Faso take a karkashin mulkin soja da su ka sha alwashin kawo karshen masu tayar da kayar baya da sunan jihadi.
Tun daga 2016 ne kungiyoyin dake dauke da makamai suke kai hare-hare a sassa mabanbanta na kasar ta Burkina Faso da sunan jihadi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025 Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Fizishkiyan: Wajibi Ne Musulmi Su Hada Kai Domin Dakatar Da Laifukan HKI September 15, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Takwarorinsa Na Kasashen Qatar, Turkiyya, Pakistan Da Labanon A Doha September 15, 2025 Kwamitin Kolin Tsron Kasar Iran Ya Amince Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma Da Hukumar IAEA September 15, 2025 Jami’in Kasar Yemen Ya Aike Da Sako Ga Mahalarta Taron Birnin Doha Na Kasar Qatar September 15, 2025 Yawan Mutanen Da Suka Yi Shahada Sakamakon Kisan Kiyashin ‘Yan Sahayoniyya A Gaza Ya Kusaci 65,000 September 15, 2025 Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces September 15, 2025 Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci