Ba abin mamaki ba ne idan na fice daga NNPP – Abdulmumin Kofa
Published: 5th, September 2025 GMT
Dan Majalisar Wakilai na mazabar Kiru/Bebeji daga jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya ce ba zai zama abin mamaki ba idan ya fice daga jam’iyyar.
Ya kuma ce da arzikinsa ya shiga tsarin Kwankwasiyya, kuma ya bauta mata da kudinsa kamar yadda ita ma Kwankwasiyyar ta taimake shi.
A tattaunawarsa da DCL Hausa ranar Alhamis, dan majalisar ya ce shekarunsa sun kai ya san abin da ya fi dacewa da shi kuma ya yankewa kansa hukunci kan abin da fi dacewa da shi.
Kofa ya ce, “Ita kanta jam’iyyar ta NNPP ta ce tana nazarin abin da ya dace da ita, saboda haka ba wai dole ne inda jam’iyyar ta nufa na ce dole ni ma can zan bi ba.
“Shekaruna sun kai inda zan iya yanke wa kaina hukunci kan abin da ya fi dacewa da ni,” in ji dan majalisar.
Sai dai ya ce Kwankwaso maigidansa ne kuma zai ci gaba da girmama shi ko suna jam’iyya daya ko ba sa tare.
“Ko ina tare da Kwankwaso ko ba ma tare, ba za ka taba ji na taba shi ba. Shi kansa Gandujen ban taba zaginsa ba don ma tare.
“Ban taba zuwa neman a ba ni kwangila ba a gwamnatin Kwankwasiyya duk da cewa da ni aka kafa ta. Kwankwasiyya ta yi min rana, amma ni ma na yi mata,” in ji shi.
Ya kuma yi zargin cewa babu wanda ya taimake shi lokacin da yake fama da rigimar dakatar da shi da aka yi lokacin da ya zargi jagorancin Majalisar Wakilai a 2016, kan rikicin zargin cushe a kasafin kudi.
Da aka tambaye shi yaushe zai bar jam’iyyar, sai ya ce, “Komai mai iya yiwuwa ne. zan iya tsayawa a NNPP, zan iya barinta, zan iya komawa APC, idan na gad ama na tafi PDP, ko ADC ko ma PRP. Duk inda nake so idan na ga dama zan tafi. A lokacin da na yanke hukunci kowa zai sani.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana, tare da amsa tambayoyin manema labarai.
A cewar bayanan da aka gabatar a yayin taron, ayyukan tattalin arzikin kasar a watan Agusta sun samu ci gaba ba tare da tangarda ba. Kuma hakan ya bayyana ne ta hanyoyi daban-daban kamar haka: masana’antu sun habaka cikin sauri, masana’antar kera kayayyakin aiki da masana’antar fasaha sun samu ci gaba mai kyau. Kana ayyukan bayar da hidima su ma sun bunkasa cikin sauri. Baya ga haka, an samu ci gaba mai kyau a bangaren bayar da hidimomi na zamani. Harkokin kasuwanci sun samu ci gaba cikin natsuwa, inda harkokin sayar da kayayyaki ga masu sayayya suka kara habaka. Har ila yau, kadarorin jari sun ci gaba da karuwa, jarin masana’antu ya habaka cikin sauri, harkokin fice da shigen kayayyaki sun ci gaba da girma, tsarin kasuwanci ya ci gaba da ingantuwa, kana yanayin samar da guraben aikin yi, ya kasance kan wani mataki mai daidaito. Sai dai kuma saboda yanayin da ake ciki, adadin marasa aikin yi a birane ya karu, ma’aunin Core CPI ya ci gaba da hauhawa, kana faduwar farashin kayayyakin masana’antu ya ragu.
Bayanan sun kara da cewa, akwai bukatar lura da cewa, ana fuskantar yanayin rashin tabbas a waje, kuma tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar kalubale da hadari da yawa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp