Leadership News Hausa:
2025-09-17@23:11:56 GMT

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Damfara A Kano

Published: 4th, September 2025 GMT

‘Yansanda Sun Kama Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Damfara A Kano

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan damfara ne da suka damfari wani tsabar kudi har Naira Miliyan N1,030,000 ta hanyar ba saja da jami’an tsaro. Wadanda ake zargin sun hada da Nasiru Adamu mai shekaru 30 daga jihar Sokoto; Yusuf Sani, 49; da Aliyu Yusuf dan shekaru 25, dukkansu daga karamar hukumar Daura ta jihar Katsina, an kama su ne a ranar 2 ga Satumba, 2025, da misalin karfe 1:30 na rana a unguwar Dan’agundi ta Kano.

Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Ƴan Ta’adda 15 A Borno Ƴan Siyasar Arewa Na Rigima Da Juna, Tinubu Na Murna — Jibrin Kakakin Rundunar, Abdullahi Kiyawa, a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Alhamis, ya bayyana cewa kamen ya biyo bayan kiran gaggawa daga wanda aka damfara, mai suna, Salisu Ibrahim. Kakakin ‘yansandan ya ce, binciken farko da aka yi ya nuna cewa wadanda ake zargin sun bayyana kansu ne a matsayin jami’an tsaro kuma sun yi ikirarin cewa suna da kwarewa ta musamman don taimaka wa wanda aka damfarar. Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun umurci Ibrahim da ya kawo kudin zuwa wani wuri inda suka yi alkawarin taimaka masa. Ya kara da cewa jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar jama’a sun yi nasarar cafke duk wadanda ake zargin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: da ake zargin

এছাড়াও পড়ুন:

NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani ɗan ƙasar Indiya tare da wasu mutane uku bisa zargin shigo da ƙwayoyin Tramadol da aka ƙiyasta darajarsu ta kai naira biliyan uku (N3bn) zuwa cikin ƙasar.

A cewar NDLEA, wannan shi ne kamen ƙwayoyi mafi girma da hukumar ta yi a cikin shekarar nan, lamarin da ke nuna yadda safarar miyagun ƙwayoyi ke ƙaruwa a ƙasar.

Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa jami’anta sun kama mutanen ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas, bayan sun samu bayanan sirri da suka taimaka wajen gano su.

NDLEA ta bayyana cewa ƙwayoyin Tramadol ɗin da aka gano an shigo da su ne cikin kwalaye a matsayin maganin multivitamins, yayin da ake ƙoƙarin fitar da su daga filin jirgin a wasu manyan motoci.

“Ƙwayoyin da aka kama ba su da wata alaƙa da amfani na lafiya, waɗanda aka shigo da su a ɓoye a matsayin maganin rage kasala da ƙara kuzari (multivitamins),” in ji sanarwar NDLEA.

Rahotanni sun nuna cewa a da likitoci na bayar da Tramadol ne don rage zafi da raɗaɗin ciwo, amma yanzu ta zamo annoba musamman a tsakanin matasa, wadda ke haddasa mummunan maye da illa ga lafiya.

Hukumar ta nuna damuwa game da yadda yawan masu amfani da Tramadol ke ƙaruwa ba wai a Najeriya kaɗai ba, har ma a wasu ƙasashen Afirka, duk da illolin da ƙwayar ke haddasawa, kamar matsalolin taɓin hankali ko ma rasa rai gaba ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin