Ƙara Kuɗin Fasfo: Gwamnati na jefa ’yan Najeriya cikin matsi — Obi
Published: 29th, August 2025 GMT
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki Gwamnatin Tarayya kan ƙara kuɗin fasfo.
Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS), ta ƙara kuɗin fasfo mai shafi 32 zuwa Naira 100,000, yayin da mai shafi 64 ya koma Naira 200,000.
Ambaliya ta raba ƙauyukan Sakkwato 6 da sauran sassan jihar An fara gyaran layin dogon Abuja-Kaduna bayan hatsarin jirgin ƙasaObi, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na X, inda ya ce wannan ƙarin ba adalci ba ne duba da halin matsin tattalin arziƙi da ake fuskanta.
“Wannan gwamnati kullum na ƙara jefa mutane cikin wahala a maimakon ta sauƙaƙa musu rayuwa,” in ji shi.
“An ƙara kuɗin fasfo sau uku cikin shekaru biyu kacal. Wataƙila Najeriya ce kaɗai ƙasar da fasfo ya fi mafi ƙarancin albashin ma’aikata yawa.”
Obi, ya ce a yanzu sai ma’aikacin gwamnati ya haɗa albashin wata biyu kafin ya samu fasfo.
Wannan sabon ƙari ya zo ƙasa da shekara guda bayan ƙarin da gwamnatin ta yi a watan Agustan 2024, lokacin da fasfo mai shafi 32 ya tashi daga Naira 35,000 zuwa Naira 50,000, yayin da mai shafi 64 ya tashi daga Naira 70,000 zuwa Naira 100,000.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Ƙara Kuɗin Fasfo wahala
এছাড়াও পড়ুন:
Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.
Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.
Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da AmurkaA cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.
“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.
Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.
“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.
Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.
Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.
“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.