Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Shigo Da Su Daga Kasashe Masu Karancin Ci Gaba Na Afrika Ya Karu Da Kaso 10.2 Cikin Watanni 7 Da Suka Gabata
Published: 29th, August 2025 GMT
Ma’aikatar kula da harkokin cinikayya ta kasar Sin ta ce daga watan Junairu zuwa Yulin bana, darajar abubuwan da Sin ta shigo da su kasar daga kasashe masu karancin ci gaba na Afrika, ta kai dala biliyan 39.66, adadin da ya karu da kaso 10.2 kan na bara.
Kakakin ma’aikatar He Yongqian ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, inda ta ce wani rahoto da asusun bada lamuni na duniya (IMF) ya fitar a baya bayan nan, ya nuna cewa, karkashin jagorancin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika ya zama wani muhimmin karfi mai ingiza ci gaban tattalin arziki a nahiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
An gudanar da taron tattaunawa na duniya kan kirkire-kirkire da bude kofa da ci gaba na bai daya, jiya Juma’a a birnin Lagos na Nijeriya. Yayin taron wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG da karamin ofishin jakadancin Sin dake Lagos suka shirya, ministan kula da harkokin matasa na Nijeriya Ayodele Olawande da shugaban CMG Shen Haixiong, sun gabatar da jawabai ta kafar bidiyo.
A cewar ministan na Nijeriya, cikin shekaru 5 da suka gabata, dubban matasan kasar sun ci gajiyar tallafin karatu da shirye-shiryen horo da na musaya da Sin ta samar, kuma wannan hadin gwiwa da ake yi a aikace ya kara fahimta da aminci tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa, a shirye ma’aikatarsa take ta karfafa hadin gwiwa da sassa masu ruwa da tsaki na kasar Sin wajen ci gaba da fadada shirye-shiryen musaya da na hadin gwiwa da suka shafi matasa.
A nasa bangare, Shen Haixiong ya ce a matsayinta na babbar kafar yada labarai dake watsa shirye shiryenta ga sassa daban daban na duniya, tashar talabijin ta CCTV dake karkashin CMG da abokan huldarta, za su yayata shawarar Sin ta jagorantar harkokin duniya da gabatar da tafarkin Sin na zamanantar da kanta da karfinta na kirkire kirkire a sabon zamani ga al’ummar duniya. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA