Ana zargin miji da kashe matarsa da duka saboda zuwa gona a makare
Published: 28th, August 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti ta tabbatar da mutuwar wata mata mai suna Ofone Modupe Alasin, a karamar hukumar Efon-Alaaye da ke jihar.
Kakakin rundunar a jihar, SP Sunday Abutu ne ya tabbatar da kisan matar, inda ya ce an kama mijinta yayin da ake ci gaba da bincike.
’Yan sanda sun ceto yara 3 da aka sace a Kaduna Ba zan tsaya takarar kowanne irin mukami ba a 2027 – El-RufaiBinciken farko-farko dai ya nuna mijin ne ya lakada wa matar tasa duka saboda ta ki zuwa gonarsu a kan lokaci.
Wani makwabcin gonar ya ce ya jiyo marigayiyar tana ihun neman taimako, amma duk da haka mijin nata ya ci gaba da nada mata na jaki.
Kazalika, wata majiya daga ’yan sanda ta ce bayan duka ne mutumin ya bukaci ta samo masa ruwa daga wani rafi da ke kusa da gona.
Sai dai a kan hanyarta ta zuywa debo ruwa a rafin, ta yanke jiki ta fadi ta mutu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.